Bidiyo: Bahagon ‘Yansanda ya yi nasara a kan Autan Kudawa

Bahagon Shagon ‘Yansanda ya kai zagayen gaba a damben gwamnan jihar Kano, bayan nasara a kan Autan Kudawa ranar Juma’a.

Sun dambata a Ado Bayero Square, ibda suka yi turmi uku ba kisa hakan ya sa Bahagon ‘Yansanda daga Arewa ya dauko yes, shi kuwa Autan Kudawa daga Kudu ya dauki no.

Wasannin da aka dambata ranar Juma’a

Bahagon Gambo daga Kudu ya buge Shagon Sanin Kurna daga Arewa

Bakwai daga Kudu ya doke Bahagon Aliyu daga Jamus

Autan Dan Bunza daga Jamus ya buge Ghali Shagon Dogon Auta daga Kudu

Garkuwan Dutse daga Kudu ya kai zagayen gaba a kan Dan Bichi daga Arewa

Leave a comment