Bellingham ya kafa tarihi a Champions League

Jude Bellingham ya zama na farko da ya ci kwallo a wasa hudun da ya fara buga wa Real Madrid a Champions League a tarihi.

Ranar Laraba Real Madrid ta casa Napoli da ci 4-2 a wasan cikin rukuni na uku a gasar ta zakaraun Turai.

Dan wasan tawagar Ingila, ya ci kwallo a minti na 22 da take leda, inda Real Madrid ta ci 2-1 a lokacin, kuma na 15 da ya zura a raga a wasa 16 a kungiyar ta Santiago Bernabeu.

Tuni dai Real ta kai zagaye na biyu a Champions League na kakar nan, Napoli ce ta biyu da maki bakwai, sai Braga mai hudu da Union Berlin mai biyu.

Ranar 12 ga watan Disamba za a kammala wasannin cikin rukuni, inda Napoli za ta kara da Braga da wanda Union Berlin za ta karbi bakuncin Real Madrid, mai Champions League 14.

Leave a comment