Bellingham da Vinicius sun taka rawa a doke Alaves

Real Madrid ta caskara Deportivo Alaves 5-0 a wasan mako na 36 a La Liga da suka kara ranar Talata a Santiago Bernabeu.

Wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Jude Bellingham da Vinicius Junior da ya zura biyu a raga da Federico Valverde da kuma Arda Guler.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta ci gaba da zama ta daya a teburin La Liga da maki 93, sai Barcelona ta biyu mai maki 76.

Barcelona ta ci gaba da zama a matakin bayan da Girona ta yi rashin nasara 1-0 a gida a hannun Villareal, kenan tana matakinta na uku da maki biyar, sai Atletico Madrid ta hudu mai maki 70.

Real Madrid, wadda ta yi bikin lashe La Liga na bana na 36 jimilla ranar Lahadi, za ta buga wasan karshe a Champions League da Borussia Dortmund ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Real mai Champions League 14 ta samu wanna matakin, bayan da ta yi waje da Bayern Munich, ita kuwa Dortmund mai kofin zakarun Turai daya, ta fitar da Paris St Germain ce.

Leave a comment