Bayern ta yi wasa 37 ba a doke ta a cikin rukuni ba

Ranar Laraba Bayern Munich za ta karbi bakuncin Galatasaray a wasa na hurhudu a rukunin farko a Champions League.

Kungiyar da ke rike da Bundesliga ta yi wasa 37 a jere a cikin rukuni ba tare da an doke ta ba a gasar zakarun Turai.

Da zarar Bayern ta yi nasara za ta samu gurbin shiga zagaye na biyu da zai rage saura karawa bibiyu a cikin rukunin farko.

Kungiyar Jamus ta je Instanbul ta doke Galatasaray 3-1 a karawar cikin rukunin farko a cikin watan Oktoba.

Wasa na baya da Bayern ta karbi bakuncin Galatasaray a Munich shi ne karawar farko a cikin rukuni a European Cup a 1972/73, inda Bayern ta ci 6-0.

Haka kuma Bayern ta yi nasara a karawa shida baya ko dai a European Cup ko kuma Champions League da kungiyoyin Turkiya, inda ta ci kwallo 21-2.

Wasan da Galatasaray ta doke Manchester United 3-2 a wasa na bibiyu a cikin rukuni, shi ne ya kawo karshen karawa 17 a jere da aka ci kungiyar a wasannin waje, wadda ta yi canajars uku aka doke ta 14.

Bayern Munich ce ta daya a rukunin farko da maki tara, sai Galatasaray da hudu da Manchester United mai uku da kuma FC Copenhagen mai daya.

Leave a comment