Bayern ta bai wa Dortmund tazarar maki tara

Bayern Munich ta caskara Union Berlin 4-0 a wasan mako na 27 a Bundesliga ranar Asabar.

Micheal Olise ne ya fara cin ƙwallo, sai Serge Gnabry da ya zura biyu a raga da kuma Harry Kane da ya ci na huɗu a wasan.

Ƙwallon da Kane ya zura a raga ta zama ta 31 a bana a Bundesliga, kenan saura 10 ya yi kan-kan-kan da tarihin da Robert Lewandowski ya kafa a cin kwallaye a 2020/21.

Da wannan sakamakon Bayern Munich, wacce wasa ɗaya aka ci a Bundesliga a kakar nan tana kan gaba a teburi da maki 70 da tazarar tara tsakani da Borussia Dortmund ta biyu.

Kane ƙyaftin ɗin tawagar Ingila, yana cikin ƴan wasan da Thomas Tuchel ya gayyata, domin fafatawa a sada zumunta da Urugauay da kuma Japan,

Sai dai kociyan tawagar Ingila ya ce Kane da wasu ƴan wasan zai hutar da su a karawa da Uruguay, amma za su fuskanci wasan Japan.

Yanzu dai Kane yana da damar kara cin ƙwallaye a wasan da Bayern za ta je Freiburg a Bundesliga ranar 4 ga watan Afirilu.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top