Bayern Munich na rarrashin Tuchel ya ci gaba da aiki

Wasu rahotanni na cewar Bayern Munich na rarrashin Thomas Tuchel ya ci gaba da horar da kungiyar, bayan da zai bar kungiyar a karshen kakar nan.

Rahoton ya ce mahukuntan Bayern Munich na fatan Tuchel zai ci gaba da jan ragamar kungiyar bayan da har yanzu ba ta samu madadinsa ba.

Jaridar Bild da Kicker sports da Sky TV duk sun bayar da rahoton cewar wani jam’in Bayern da darakta, Christoph Freund suna tattaunawa da Tuchel don kulla wata matsayar.

Haka kuma Bild ta bayyana wakilin Tuchel, Olaf Meinking a hedikwatar Bayern Munich.

Tuchel, wanda ya ja ragamar Chelsea ta lashe Champions League a 2021, ya maye gurbin Julian Nagelsmann a cikin Maris din 2023 kan kwantiragin da za ta kare a 2025.

Sai dai kungiyar ta ci karo da koma baya a wasannin da take buga wa, hakan ya sa mahukuntan kungiyar da Tuchel suka cimma matasaya cikin Fabrairu da cewar ya hakuri da aikin da zarar an kammala kakar nan.

Kawo yanzu Bayern ta kasa samun kociyan da za ta bai wa aikin a kakar badi, bayan da ta tuntubi Xabi Alonso da Ralf Rangnick da kuma Nagelsmann, wadanda suka ce ba za su iya barin aikin da suke kan yi ba.

Rahotannin na cewar manyan ‘yan wasan Bayern da suka hada da Manuel Neuer da Thomas Müller da Harry Kane da kuma Jamal Musiala, duk suna son Tuchel ya ci gaba da horar da kungiyar.

To sai dai Tuchel ya ce koda zai ci gaba sai ya samu goyon bayan dukkan mahukuntan Bayern har da shugaba, Uli Hoeness wanda ya zargi kocin da sayen manyan ‘yan wasa da tsada maimakon ya reni matasan kungiyar.

Haka kuma Tuchel zai bukaci kunshin kwantiragi mai tsayo da za ta kai ya samu damar nuna kwarewarsa a kungiyar.

Leave a comment