Bayern Leverkusen ta yi wasa na 48 a jere ba a doke ta ba

Bayern Leverkusen ta je ta doke Eintracht Frankfurt 3-1 a gasar Bundesliga ranar Lahadi, wasa na 48 a jere a dukkan karawa ba a doke ta ba.

Tuni dai Leverkusen ta lashe Bundesliga na bana na farko a tarihi, bayan shekara 120 da aka kafa kungiyar, wadda ta takawa Bayern Munich burki, wadda ta lashe 11 a jere.

Xabi Alonso ya kalli wasan a cikin ‘yan kallo bayan katin gargadi da aka dakatar da shi, inda Leverkusen ta ci kwallaye ta hannun Granit Xhaka da Patrik Schick da Jeremie Frimpong da Exequiel Palacios da kuma Victor Boniface.

Leverkusen na fatan kafa tarihin ta farko da ta buga Bundesliga kaka gabaki ba tare da an doke ta ba, idan har ba ta yi rashin nasara ba a karawa biyun da ta rage mata.

Kungiyar na fatan lashe kofi uku a bana, bayan da ta doke Roma 2-0 a Italy ranar Alhamis a wasan farko na daf da karshe.

Haka kuma za ta buga wasan karshe a German Cup da Keiserslauten.

Leave a comment