Bayern da Real sun tashi 2-2 a Champions League a Germany

Bayern Munich da Real Madrid sun tashi 2-2 a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Allianz Arena.

Vinicius Junior ne ya fara ci wa Real kwallon farko, sannan ya ci na biyu a bugun fenariti, bayan da Kim Min-jae judo ya yi wa Rodrygo keta a cikin da’ira ta 18.

Leroy Sane ya fara ci wa Bayern Munich daga baya Harry Kane ya kara na biyu a bugun fenariti, wanda ya zura kwallo 35 a Bundesliga a kakar farko da yake yi daga Tottenham.

Da wannan sakamakon sai a wasa na biyu ranar Laraba 8 ga watan Mayu za a tantance wadda za ta kai wasan zayaen karshe a Santiago Bernabeu.

Wannan shi ne wasa na 27 da suka kece raini a tsakaninsu, inda Real ta ci 12, Bayern ta yi nasara 11 da canjaras hudu.

Real Madrid tana da Champions League 14, yayin da Bayern Munich keda kofin zakarun Turai shida.

Leave a comment