Bayanai kan wasan Chelsea da Crystal Palace

Chelsea za ta karbi bakuncin Crystal Palace a wasan mako na 19 a Premier League ranar Laraba a Stamford Bridge.

A bara da kungiyoyin biyu suka kara, Chelsea ta je ta doke Palace 2-1 a Selhurst Park ranar 1 ga watan Oktoban 2022.

Ranar 15 ga watan Janairun 2023, Chelsra ta yi nasara da ci 1-0 a Stamford Bridge.

Chelsea tana ta 11 a teburin Premier League da maki 22, Palace kuma mai maki 18 tana ta 15 a kasan teburin.

Chelsea na sa ran Moises Caicedo ko zai iya buga mata wasan, bayan da ya yi rashin lafiya.

Ana sa ran Raheem Sterling da Cole Palmer za su buga fafatawar, amma Enzo Fernandez da Lesley Ugochukwu na jinya.

Crystal Palace na fatan Odsonne Edouard ya buga mata wasan na ranar Laraba, wanda ya yi jinyar raunin gwiwa.

‘Yan kwallon da ke jinya a Palace sun hada da Sam Johnstone da Joel Ward da Rob Holding da Cheick Doucoure da kuma Jesurun Rak-Sakyi.

Chelsea da Crystal Palace

Crystal Palace ta yi rashin nasara 11 a jere a wasa da Chelsea.

Chelsea ta doke Palace a karawa shida baya a Stamford Bridge ba tare da an zura mata kwallo ba a raga a hudu daga ciki.

Babu canjaras a fafatawa 24 baya da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu a Premier League.

Chelsea

Chelsea ta yi nasara biyu a jere a gida, fiye da nasarar da ta samu a fafatawa 17.

Rabon da ta ci wasa uku a jere tun bayan Agusta zuwa Oktoban bara.

Amma ta kasa nasara a gida a karawa hudu a wasan hamayya da kungiyoyin Landan – tun bayan doke Crystal Palace cikin Janairu ta yi rashin nasara biyu da canjaras biyu daga ciki.

Amma ba ta yi wasa biyar ba tare da nasara ba a fafatawar hamayya da kungiyoyin Landan a Stamford Bridge tun1995-96.

Idan aka doke Chelsea zai zama rashin nasara 24 a dukkan karawa a 2023, kwazo mafi muni kenan tun bayan 1978.

Mauricio Pochettino ya lashe wasa biyar a Premier League a matakin koci a Tottenham da ya fuskanci Roy Hodgson na Crystal Palace da cin kwallo 9-0.

Crystal Palace

Wasa daya Crystal Palace ta ci daga 11 a Premier League a bayan nan shi ne 2-0 da ta je ta doke Burnley ranar 4 ga watan Nuwamba ta yi rashin nasara shida da canjaras hudu.

Kungiyar da Roy Hodgson ke jan ragama ba ta yi nasara a karawa shida da take buga wasa a tsakiyar mako ba a 2023, an doke ta hudu da canjaras biyu ba ta zura kwallo ba a raga a wasannin.

Wasa daya ta ci daga 13 a Premier League a karawar hamayya ta kungiyoyin Landan, shi ne 4-3 da ta doke West Ham United cikin Afirilu, an doke ta karo bakwai daga ciki da canjaras biyar.

Leave a comment