Barcelona za ta kara da Almeri a La Liga ranar Alhamis

Barcelona za ta je gidan Almeri, domin buga wasan mako na 36 a gasar La Liga ranar Alhamis.

Wannan shi ne karo na biyu da za su kara a gasar, bayan da Barcelona ta ci 3-2 ranar 30 ga watan Disambar 2023.

Kuma wadanda suka ci mata kwallayen sun hada da Raphinha da kuma Sergio Roberto da ya ci biyu a wasan.

Barcelona tana ta biyun teburi da maki 76, yayin da Almeri ta karshen teburin kakar bana take ta karshe ta 20 da maki 17.

Tuni dai kociya, Xavi Hernandez ya bayyana ‘yan wasan da suka je Almeria.

‘Yan wasan Barcelona:

Ter Stegen, João Cancelo, Íñigo Martínez, Ferran Torres, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix da kuma Christensen.

Sauran sun hada da Fermín, Marcos Alonso, Romeu, Vitor Roque, Sergi Roberto, Kounde, Lamine Yamal, Marc Casadó, Kochen, Cubarsí da kuma Héctor Fort

Tuni dai Real Madrid ta lashe La Liga na bana na 36, wadda take da maki 93 a wasa 36 da ta buga, Girona tana ta ukun teburi da tazarar maki daya tsakani da Barcelona da kuma Atletico Madrid ta hudu da maki 73.

Haka a ranar ta Alhamis za a buga wasan mako na 36 tsakanin Real Sociedad da Valencia da kuma wasan mako na 37 da za a kara tsakanin Las Palmers da Real Betis.

Real Madrid za ta buga wasan karshe a Champions League da Borussia Dortmund ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Real Madrid mai kofin zakarun Turai 14 ta kai wasan karshe ne, bayan yin waje da Bayern Munich.

Ita kuwa Dortmund mai Champions League ta yi waje da Paris St Germain.

Wasannin La Liga da za a buga ranar Alhamis

  • Las Palmas da Real Betis         
  • Almeria da Barcelona
  • Real Sociedad da Valencia

Leave a comment