Barcelona ta koma ta uku bayan cin Atletico

Barcelona ta doke Atletico Madrid da cin 1-0 a wasan mako na 15 a La Liga ranar Lahadi.

Kungiyar da Xavi ke jan ragama ta ci kwallon a minti na 28 ta hannun Joao Felix.

Wannan shi ne karo na hudu da Barcelona ta ci 1-0 a La Liga a bana, wadda ta ci uku a gida da daya a waje.

Barcelona, wadda ke fama da ‘yan wasan da ke jinya ta ci kwallo 28 a La Liga kawo yanzu, an zura mata 14 a raga.

Da wannan sakamakon Barcelona ta koma mataki na ukun teburi da maki 34, ita kuwa Atletco mai kwantan wasa ta koma ta hudu da maki 31.

Real Madrid ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 38, iri daya da na Girona ta biyu.

Jadawalin wasannin mako na 16:

Ranar Juma’a 8 ga watan Disamba

  • Getafe da Valencia

Ranar Asabar 9 ga watan Disamba

  • Deportivo Alaves da Las Palmas     
  • Real Betis da Real Madrid
  • Villarreal da Real Sociedad     
  • Real Mallorca da Sevilla

Ranar Lahadi 10 ga watan Disamba

  • Atletico Madrid da Almeria    
  • Granada da Athletic de Bilbao        
  • Cadiz da Osasuna   
  • FC Barcelona da Girona

Leave a comment