Barcelona ta koma ta biyu a teburin La Liga

Barcelona ta koma ta biyu a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Valencia 4-2 a wasan mako na 33 ranar Litinin.

Barcelona ta fara cin kwallo a minti na 22 da take leda ta hannun Femin Lopez, sai dai minti biyar tsakani Hugo Duro ya farke, sannan Pepelu ya ci wa Valencia na biyu a bugun fenariti.

Sai dai Valecia ta karasa karawar da ‘yan kwallo 10 a cikin fili, sakamakon jan kati da aka bai wa mai tsaron raga, Giorgi Mamardashvili daf da za su je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Robert Lewandowski ya farke kwallo, sannan ya kara biyu, wato ya ci uku rigis a karawar.

Da wannan sakamakon Barcelona mai rike da kofin bara tana ta biyun teburi da maki 73 da tazarar 11 tsakani da Real Madrid mai shirin lashe La Liga na bana na 36 jimilla.

Girona ce ta biyu da maki 71, bayan buga wasa 33, sauran karawa biyar a karkare kakar La Liga ta bana.

Ranar Asabar za a buga wasan hamayya tsakanin Girona da Barcelona a La Liga, inda aka doke Barcelona a wasan farko.

Gurbi na biyu a teburin La Liga kan bayar da damar buga Spanish Super Cup da ake yi tsakanin wadanda suka kai wasan karshe a Copa del Rey da wadda ta yi ta daya da ta biyu a teburin La Liga.

Leave a comment