Barcelona ta je ta ci PSG a Champions League

Paris St Germain ta yi rashin nasara a hanun Barcelona da ci 3-2 a wasan farko zagayen quarter finals ranar Talata a France.

Minti na 37 da fara wasa Barcelona ta ci kwallo ta hannun Raphinha, kuma haka suka je hutu kungiyar da Xavi ke jan ragama tana da cin 1-0.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Paris St Germain ta farke ta hannun Ousmane Dembele, sannan Vitinha ya kara na biyu.

Bayan da wasa ya nutsa ne Barcelona ta farke ta hannun Raphinha, sannan Andreas Christensen ya kara na uku a raga.

Ranar Talata 16 ga watan Afirilu Barcelona za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu a Champions League zagayen daf da na kusa da na karshe a Spain.

Sai dai kafin nan Barcelona wadda take ta biyu a teburin La Liga za ta je gidan Cadiz domin buga babbar gasar tamaula ta England ranar Asabar 13 ga watan Maris.

PSG kuwa wadda take jan ragamar teburin Ligue 1 ba ta da wani wasan a gabanta in banda zuwa Barcelona domin buga zagaye na biyu a Champions League ranar Talata 16 ga watan Afirilu.

Daga nan ne za ta karbi bakuncin Lyon a gasar Ligue 1 ranar Lahadi 21 ga watan Afirilu.

Leave a comment