Barcelona ta doke Alaves tana nan mataki na uku a la liga

Barcelona ta doke Deportivo Alaves 2-1 a wasan mako na 13 a gasar La Liga da suka kara ranar Lahadi a Olimpic Lluis Companys..

Minti daya da take leda Alaves ta ci kwallo ta hannun Samu, kuma haka suka je hutu ana cin Barcelona kwallo daya.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Robert Lewandowski ya farke, sannan ya kara na biyu.

Barcelona ta ci gaba da zama ta uku a kan teburin La Liga da maki 30, ita kuwa Alaves mai mai maki 12 tana ta 14.

Girona ce ta daya da maki 34, bayan karawa 13, sai Real Madrid mai maki 32 a mataki na biyu a teburin La Liga na bana.

Leave a comment