Barcelona ta ci kwallo 200 karkashin xavi

Kungiyar Barcelona ta ci kwallo 200 karkashin koci, Xavi Hernandez tun bayan da ya karbi aikin horar da kungiyar.

Robert Lewandowski ne ya ci na 200 a kwallo na biyu da ya ci a karawar da Barca ta doke Alaves 2-1 a wasan La Liga ranar Lahadi.

Wasa 107 Xavi ya ja ragama Barcelona kenan, yayin da aka zura kwallo 103 a ragar kungiyar.

Cikin kwallayen da Barca ta ci Lewandowski ne ya zura 41, sai Ferran Torres mai 19 da Pedri da Aubameyang masu 13 kowanne da Ansu Fati da Raphinha kowanne da 12 da kuma Dembélé mai 10.

Haka kuma Lewandowski ne ya ci kwallo na 100 a karkashin Xavi, shi ne na uku a 4-0 da Barca ta doke Athletic Club cikin Oktoban 2022.

Cikin wasa 107 da Xavi ya ja ragama kawo yanzu ya yi nasara a 67 da canjaras 19 aka doke shi wasa 21.

Ter Stegen shi ne kan gaba a yawan buga wa Barca tamaula karkashin Xavi, wanda ya yi wasa 102, sai Gavi na biyu da ya buga fafatawa 97.

Leave a comment