Barcelona na fatan buga Spanish Super Cup a badi

Barcelona ta koma mataki na biyu a teburin La Liga, bayan da ta doke Real Sociedad 2-0 a wasan mako na 35 ranar Litinin.

Barcelona ta fara cin kwallo ta hannun Lamine Yamal daga ta kara na biyu ta hannun Raphinha a bugun fenariti.

Mai tsaron ragar Sociedad, Remiro ya hana kwallaye da dama ya shiga ragarsa, har da wani mai kyau da Raphinha ya buga masa.

Da wannan sakamakon kungiyar da Xavi ke jan ragama tana ta biyu da tazarar maki 14 tsakani da Real Madrid ta daya da tazarar maki daya tsakani da Girona, wadda ta yi kasa zuwa mataki na uku, kuma saura wasa uku-uku a karkare kakar bana.

To sai watakila Girona ta koma mataki na biyu ranar Talata, wadda za ta karbi bakuncin Villareal a wasan mako na 37 da za ta fafata.

Barcelona na fatan samun gurbin na biyu, domin ta buga Spanish Super Cup na badi.

Ana buga Spanish Super Cup ne tsakanin wadda ta lashe La Liga a kakar da wadda ta yi mata da biyu da kuma biyun da suka buga wasan karshe a Copa del Rey.

Leave a comment