Barcelona na duba yadda za ta kara daukar Enrique

Barcelona na duba yiwuwar sake daukar kociyan Paris St-Germain, Luis Enrique, domin maye gurbin Xavi a 2025. (Sport – in Spanish)

Manchester United ba ta shirya korar Erik ten Hag ba tun kan wasan karshe a FA Cup franar 25 ga watan Mayu. (Telegraph – subscription required)

Sai dai watakila a kori Ten Hag da zarar an kammala kakar bana. (Football Insider)

Kociyan Bayern Munich, Thomas Tuchel wanda zai bar kungiyar a karshen kakar bana, yana sha’awar karbar aiki jan ragamar Manchester United idan ta yanke shawarar Ten Hag. (Telegraph – subscription required)

Tsohon kociyan Manchester United, Jose Mourinho na son ya sake karbar aikin horar da kungiyar karo na biyu, amma kungiyar ba ta nuna sha’awar sake daukarsa ba. (Manchester Evening News)

Crystal Palace ta shirya sayar da Marc Guehi, maimakon cefanar da Michael Olise ko Eberechi Eze a karshen kakar bana. (Givemesport)

Chelsea na neman wadda za ta sayi Armando Broja, wanda ya buga wasannin aro a Fulham. (Fabrizio Romano)

Shugaban Barcelona, Joan Laporta ya tuntubi Getafe don tantance halin da dan wasan Manchester United ke ciki mai buga wasannin aro a kungiyar Mason Greenwood. (Radio Marca, via Mundo Deportivo – in Spanish)

Newcastle da Inter Milan sun shiga sawun masu son daukar dan wasan Barcelona, Jules Kounde, wanda Chelsea da Manchester United da kuma Paris St-Germain ke bibiya. (Mundo Deportivo – in Spanish)

Leave a comment