Barau FC ta samo maki a Wikki Tourist

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barau FC ta je ta tashi 0-0 a wasan mako na 31 a Premier ta Nigeria ranar Asabar,

Shi ne wasan da aka fara yi a makon nan daga 10 da ake sa ran za a buga, kenan za a karkare sauran taran ranar Lahadi.

Da wannan sakamakon Barau FC ta koma ta taran teburi da maki 41 daga wasa 31 da ta buga.

Karo na 11 da Barau FC ta buga canjaras a kakar nan da cin wasa 10 aka doke ta 10 daga ciki.

A mako mai zuwa Barau FC za ta karɓi bakuncin Katsina United a karawar mako na 32 a filin wasa na Sani Abacha Stadium a Kano.

Wasannin da za a buga a Premier ranar Lahadi:

  • Kano Pillars da Enyimba
  • Enugu Rangers da El-Kanemi Warriors
  • Katsina United da Shooting Stars
  • Kun Khalifat da Ikorodu City
  • Plateau United da Bayelsa United
  • Remo Stars da Kwara United
  • Warri Wolves da Beldel Insurance
  • Abia Warriors da Niger Tornadoes
  • Nasarawa United da Rivers United

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top