Ban samu goyon baya a Man United kamar Ten Hag ba – Maurinho

Jose Mourinho ya ce ya gudanar da aiki a Manchester United da aka samu nasarori, amma bai samu goyon baya kamar yadda ake yi wa Erik Ten Hag ba.

Mourinho ya lashe League Cup da Europa League a kakarsa ta farko da ya fara aiki a Old Trafford, sannan ya yi na biyu a teburin Premier Leagu a kaka ta biyu.

Sai dai dan kasar Portugal ya ce ya ci karo da kalubale da yawa sakamakon aikin da ya yi karkashin babban jami’in United, Ed Woodward, wanda ya sallami kociyan cikin Disambar 2018, bayan kasa tabuka abin gani a sakamakon wasannin.

Sai dai an dan samu ci gaba a Manchester United mai Premier League12, tun bayan barin Jose Mourinhho, aka maye gurbinsa da Ten Hag, bayan da Ole Gunner Solskjaer da Ralf Rangnick suka kasa tabuka abin kirki.

Tsohon kociyan Chelsea da Inter Milan da Real Madrid ya koma aiki a horar da tamaula a Premier League a Tottenham a 2019 daga nan ya koma Roma a Janairu.

Mourinho ya ce yana kaunar United, yana fatan ta yi nasara a duk lokacin da take buga wasanninta.

Ten Hag, wanda ya dauki Carabao Cup a kakar farko a United da kai kungiyar Champions League a bana, wanda ya karbi aiki ranar 1 ga watan Yuli ya ja ragamar wasa 107 da cin 62 da canjaras 16 aka doke shi 29.

Leave a comment