Bakwai ya kashe Dogon Shamsu a damben Kano

Gaba bakwai ya kashe Dogon Shamsu a damben kasuwa da suka buga ranar Alhamis a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano, Nigeria.

Bakwai dan damben Kudu ya yi nasara a kan Dogon Shamsu daga Arewa a turmi na biyu.

Sauran sakamakon damben da aka buga an tashi cnajaras tsakanin Ramadan daga Arewa da Dan Butsalle daga Kudu, Autan dan Bunza daga Jamus da Garkuwan Cindo Guramada da na Shagon Bahagon ‘Yansanda daga Arewa da Soja wuta – wuta Guramada.

Kafin nan an buga wasu damben gasar gwamnan Kano.

Leave a comment