Ba za a hukunta Arteta ba kan sukar rafli

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ba za ta hukunta kociyan Arsenal, Mikel Arteta ba, wanda ya yi kalamai kan ingancin alkalan Premier League.

Lamarin ya faru ne bayan tashi wasan da Newcastle United ta ci Gunners 1-0 a wasan Premier League a watan jiya.

Ran Arteta ya baci matuka kan kwallon da Anthony Gordon ya ci Gunners a St James Park, wanda ya kwatanta alkalancin da ‘’abin kunya da ban takaici.’’

Tun farko an bukaci Arteta ya kare kansa, bayan da FA ta tuhumeshi daga baya ta ce ba ta samu wata kwakkwarar shaida ba.

Kociyan ya yi hira da ‘yan jarida, inda ya tuhumi ingancin alkalan gasar Premier League da cewar zai ci gaba da magana a kansu, idan an yi masa rashin kyautawa.

Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Newcastle United da ci 1-0 ranar 4 ga watan Nuwamba.

Leave a comment