Ba kisa tsakanin Dan Aliyu da Autan na Aisha

Dan Aliyu da Autan na Aisha sun yi turmi uku ba kisa ranar Lahadi a damben naira 100,000.

Sun kara a wasan safe a ‘yan tifa a Marabar ‘Nyanya gidan wasa na Idris Bambarewa da ke jihar Nasarawa, Nigeria.

Turmi uku suka yi ba tare da kisa ba, inda Idris Bambarewa ya bukaci a raba su.

Sakamakon wasannin da aka yi kisa:

  • Bahagon Ali Yaro ya buge Shagon Dan Aliyu
  • Bahagon Dan Shago ya doke Shagon Terminator
  • Usha ya yi nasara a kan Shagon Basiru

Wasannin da aka yi canjaras kuwa:

  • Shagon Fatalwa da Garkuwan Yahaya
  • Dan Yalon Tula da Rabe Bahagon Ebola
  • Dogon Inda da Bahagon Yahaya
  • Ilele da Garkuwan Yahaya
  • Dogon Maiduguri da Na Jimama.

Leave a comment