Awoniyi ba zai buga wasan Nigeria da Zimbabwe ba

Dan kwallon Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi ya koma kungiyarsa, bayan raunin da ya ji a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

Najeriya ta tashi 1-1 da Lesotho a wasan farko a rukuni na uku ranar Alhamis a Uyo da ke Akwa Ibom.

Tawagogin biyu sun buga wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026 a Canada da Mexico da kuma Amurka.

Da Awoniyi aka fara karawar, amma sai sauya shi aka yi a minti na 59 da dan kwallon Nice, Terem Moffi.

Kenan ba zai yi wa Nageriya wasan da za ta buga na biyu a cikin rukuni na uku da Zimbabwe ba ranar Lahadi a Rwanda.

Ita dai Zimbabwe tana buga wasanninta a Rwanda, bayan da ba ta da katafaren filin wasa da yake da darajar da ake bukata.

Tun a ranar Juma’a Awoniyi ya koma Ingila, domin a auna girman raunin da ya ji a ranar Super Eagles ta je Rwanda.

Najeriya tana fama da ‘yan wasan da ke jinya da suka hada da Victor Osimhen da Wilfred Ndidi da kuma Samuel Chukwueze.

Leave a comment