Bidiyo: Autan Dan Bunza ya kashe Ghali a damben gwamnan Kano

Autan Dan Bunza ya kai zagaye na biyu a damben gwamnan Kano ranar Juma’a, bayan da ya doke Ghali Shagon Dogon Autan Auta.

Auta dan damben Jamus ya yi nasara a kan Ghali daga Kudu a turmin farko a filin wasa na Ado Bayero Square da ke Kano, Nigeria.

Sauran sakamakon damben da aka buga ranar Juma’a

  • Bahagon Gambo daga Kudu ya buge Shagon Sanin Kurna daga Arewa
  • Bakwai daga Kudu ya doke Bahagon Aliyu daga Jamus
  • Garkuwan Dutse daga Kudu ya kai zagayen gaba a kan Dan Bichi daga Arewa
  • Bahagon Shagon ‘Yansanda ya wuce zagayen gaba a kan Autan Kudawa

Leave a comment