Atletico ta samu dama a kan Dortmund a Champions League

Borussia Dortmund ta yi rashin nasara a gidan Atletico Madrid da ci 2-1 a wasan farko a Champions League zagayen quater finals ranar Laraba.

Minti na hudu da fara wasan ne Atletico ta fara zura kwallo a raga ta hannun Rodrigo de Paul, haka kuma Samuel Leno ya kara na biyu tun kan hudu.

Bayan da aka kusan tashi daga karawar ce Dortmund ta farke daya ta hannun Sebestien Haller.

Da wannan sakamakon Atletico Madrid wadda take ta hudun teburin La Liga za ta je Germany ranar Talata 16 ga watan Afirilu, domin buga wasa na biyu a Champions League.

Sai dai kafin nan Atletico za ta karbi bakuncin Girona ranar Lahadi 21 ga watan Afirilu, domin karawa a babbar gasar tamaula ta Spain.

Ita kuwa Dortmund ba ta da wani wasan sai ranar da za ta karbi bakuncin Atletico ranar 16 ga watan Afirilu, bayan nan ta karbi bakuncin Bayern Leverkusen a Bundesliga ranar Lahadi 21 ga watan Afirilu.

Leave a comment