Atletico Madrid za ta hutar da ƴan wasa a wasan Real Madrid a La Liga

Ranar Lahadi za a buga wasan hamayya na ƴan birnin Madrid tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid a gasar La Liga.

Za su fafata ne a wasan mako na 29, inda Real Madrid ke matsayi na biyu da maki 63, yayin da Atletico Madrid ke matsayi na huɗu da maki 57.

Manyan ƙungiyoyin Sifaniya biyu na shirin buga wannan wasa mai muhimmanci ne bayan sun samu nasara a gasar UEFA Champions League, inda suka kai matakin kwata fainal.

Real Madrid ta fitar da Manchester City, kuma za ta fafata da Bayern Munich a mataki na gaba. Ita kuwa Atletico Madrid za ta kara da FC Barcelona bayan ta fitar da Tottenham Hotspur.

Rahotanni sun nuna cewa Atletico na duba yiwuwar hutawa da wasu ‘yan wasanta domin su kasance cikin koshin lafiya, ganin cewa tana da jerin wasanni masu zafi a gaba.

Bayan wannan wasa da Real Madrid, Atletico za ta karɓi bakuncin Barcelona a La Liga, kafin ta je filin Barcelona domin buga wasan farko na kwata fainal a Champions League. Daga nan kuma za ta kara da Sevilla FC a gasar La Liga.

A halin yanzu, Atletico na fama da matsalar ƴan wasa da ke jinya, ciki har da Pablo Barrios da Jan Oblak.

Har yanzu ba a tabbatar ba ko Marc Pubill zai buga wasan da za su yi da Real Madrid a ranar Lahadi.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top