Atletico da Barca sun tsira daga hukuncin UEFA kan Vinicius

Atletico Madrid da Barcelona sun tsira daga hukuncin da hukumar kwallon Turai, UEFA ta so dauka a kansu, kan cin zarafin Vinicius Junior a Champions League a watan jiya.

Dan wasan Real Madrid ya bukaci hukumar ta dauki mataki kan cin zarafin ‘yan wasa, kafin karawar ‘yan 16 a wasa tsakanin Inter Milan da Napoli.

Sai dai wata takadda da hukumat ta fitar cikin makon nan, ba ta fayyace daukar hukunci ko mataki kan korafin da aka shigar a gabanta ba kan batun cin zarafi ‘yan wasa.

Illa dai hukumar ta Uefa ta ci tarar Atletico $5,365 kan samun magoya baya da laifin shiga fili a lokacin Champions League.

An dauki hoton magoya bayan Atletico da na Barcelona suna rera wakar cin zarafi Vinicius a filayensu, amma dai Uefa ta ce tana ci gaba da duba lamarin.

Ranar 15 ga watan Maris Real Madrid ta shigar da korafi ga mahukuntan Spain kan cin zarafin da ake yi wa matashin mai shekara 23.

Vinicius ya sharbi kuka a wajen ganawa da ‘yan jarida ranar 25 ga watan Maris lokacin da aka tambaye shi ko yaya yake ji da irin wariya da ake yi masa a filaye.

Leave a comment