Atalanta ta kai wasan karshe a Europa League a karon farko

Atalanta ta doke Merseille 3-0 ta kai wasan karshe a Europa League, bayan da suka buga wasa na biyu a daf da karshe ranar Alhamis a Italy.

Minti na 30 da fara wasa Atalanta ta fara cin kwallo ta hannun Ademola Lookman, haka suka je hutu ana cin Marseille 1-0.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne kungiyar Italy ta kara na biyu ta hannun Matteo Ruggeri, sannan El Bilal Toure ya kara na uku daf da za a tashi.

Atalanta ce ta yi waje da Liverpool a Europa League a zayaen daf da na kusa da na karshe, bayan da ta ci 3-0 a Anfield.

Da wannan sakamakon Atalanta za ta buga wasan karshe da Bayern Leverkusen ranar 22 ga watan Mayu a Dublin a filin wasa na Aviva.

Leverkusen wadda ta doke Roma ta kai zagayen karshe, ta yi wasa 49 a jere ba tare da an doke ta ba a kakar nan.

Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama ta dauki Bundesliga na farko a tarihinta a bana, bayan da ta hana Bayern Munich lashe na 12 a jere.

Haka kuma Leverkusen za ta kara da Keiserslauten a wasan karshe a German Cup.

Leave a comment