Aston Villa ta tsawaita kwantiragin Emery zuwa 2027

Aston Villa da Unai Emery sun kulla yarjejeniyar ci gaba da aiki a Villa Park har zuwa karshen kakar 2027.

Aston Villa ta dauki Emery cikin Nuwambar 2022 bayan korar Steven Gerrard, lokacin da kungiyar ke mataki na 16 a kasan teburin Premier League.

Villa ta kare a mataki na bakwai a bara karkashin Emery, hakan ya sa ta samu gurbin Europa Conference League, kuma na farko a gasar Turai tun 2010–11.

A kakar bana tana ta hudu a teburin Premier League, kuma daf take ta samu gurbin Champions League – ta bai wa Tottenham ta biyar tazarar maki shida, mai kwantan wasa biyu, wannan ci gaba ta samu.

A kwarewar da Emery keda ita ya kai Villa daf da karshe a Conference League, wadda za ta kara da Olympiakos da fatan kai wa zagayen karshe a gasar Turai a karon farko tun 1982, shima nan ci gaba ne.

Emery ya lashe Europa League uku tare da Sevilla, ya kuma dauki daya a Villarreal.

Ya horar da Arsenal wata 18, wadda ya kai Gunners mataki na biyar a teburin Premier League da kai wa wasan karshe a Europa League, inda Chelsea ta yi nasara.

Ya hada maki 115 a Premier League tun bayan da ya karbi aikin horar da Villa, kociyan da suke gabansa a wannan kwazon sun hada da na Manchester City da na Arsenal da kuma na Liverpool.

Leave a comment