Aston Villa ta samu gurbin Champions League a karon farko

Aston Villa ta samu gurbin shiga Champions League a badi, bayan da Tottenham ta yi rashin nasara a hannun Manchester City ranar Talata.

City ta je ta doke Tottenham a kwantan wasan mako na 34, hakan ya sa ta koma ta dayan teburi da tazarar maki biyu tsakani da Arsenal, saura wasan karshe ya rage ranar Lahadi.

Tottenham ce kadai wadda take mataki na biyar a teburi za ta iya karbar mataki na hudu a hannun Aston Villa, amma yanzu a ba ta tazarar maki biyar, biye da kungiyar da Unai Emery ke jan ragama, kuma ranar Lahadi za a gama Premier League.

Aston Villa ba ta taba zuwa gasar zakarun Turai ba tun bayan da aka sauya fasalin wasannin daga European Cup zuwa Champions League a1991-92.

Rabon da su buga European Cup shekara 41 tun daga1982-83 wadda ta lashe kofin a kakar 1981/82.

Aston Villa ta taba karewa a mataki na biyu a Premier League a 1992/93 da kuma mataki na hudu a 1995/96, wanda a wancan lokacin wadda ta lashe kofin ce ke zuwa buga babbar gasar tamaula ta Turai..

Leave a comment