Arsenal za ta dauki Pickford madadin Ramsdale a badi

Arsenal na duba yadda za ta dauki golan Everton, Jordan Pickford, da zarar an kammala kakar bana, domin ya taimaka mata daukar Champions League a badi. (Teamtalk)

Dan wasan Manchester City, Yan Couto, wanda ke buga wasannin aro a Girona, yana cikin ‘yan wasan da Bayern Leverkusen, da Juventus da wasu daga Premier League ke son daukar idan an kare kakar nan. (Talksport)

Graham Potter ya barar da damar karbar aikin horar da Ajax, bayan da ake ta rade-radin cewar shi ne za a bai wa aikin horar da kungiyar Dutch. (Athletic – subscription required)

Chelsea za ta tattauna da Mauricio Pochettino domin fayyace makomarsa da zarar ta kammala wasan karshe a Premier ta bana da Bournemouth. (Telegraph)

Arsenal na son zawarcin Wojciech Szczesny ko Jason Steele ko kuma Diant Ramaj, domin maye gurbi Aaron Ramsdale, wanda ake sa ran zai bar Gunners a karshen kakar bana. (Standard)

Gunners na sa ran daukar mai tsaron baya da mai buga tsakiya, domin ta kara karfin kungiyar, domin Mikel Arteta ya samu fitattun ‘yan wasan da zai bukata a badi. (Standard)

Bayern Munich ta fara tattaunawa da tsohon kociyanta, Hansi Flick domin ya sake jan ragamar kungiyar don maye gurbin Thomas Tuchel. (Sky Sports Germany)

Newcastle United na ci gaba da tuntbar Crystal Palace a shirin da take na son daukar Dougie Freedman da kuma Johannes Spors, domin zama daraktan wasannin kungiyar. (Sky Sports)

Manchester City ta amince ta dauki matashi daga Amurka, Cavan Sullivan, wanda ya koma buga Major League Soccer daga Philadelphia Union, bayan da ya cika shekara 18 da haihuwa. (ESPN)

Leave a comment