Arsenal ta koma mataki na daya a teburin Premier

Arsenal na ci gaba da fatan lashe Premier League na bana, bayan da ta je Old Trafford ta ci Manchester United 1-0 a wasan mako na 37 ranar Lahadi.

Leandro Trossard ne ya ci kwallon a minti na 20 da ya bai Gunners damar darewa kan teburi da tazarar maki daya tsakani da Manchester City, wadda ta ci Fulham ranar Asabar.

Damar yanzu tana hannun City, wadda take da kwantan wasa daya da karawar karshe da za ta yi, bayan da Arsenal ya rage mata karawa daya a gabanta.

Duk da haka kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ta ci gaba da sa matsi ga City, wadda za ta je gidan Tottenham ranar Talata a kwantan mako na 34.

Doke United da Arsenal ta yi ya sa damar zuwa kungiyar gasar zakarun Turai na dusashewa.

Kenan United tana ta takwas din teburi da tazarar maki uku tsakani da Newcastle United ta shidan teburi, wadanda za su fafata a tsakaninsu ranar Laraba.

Tun da aka shiga shekarar 2024 Arsenal ke ta kokarin gani ta lashe Premier na bana, wadda rabonta da shi shekara 20.

Arsenal ta lashe a wasa 15 da canjaras daya aka doke ta karawa daya daga 17 da ta buga tun da aka shiga sabuwar shekara.

Leave a comment