Arsenal ta kai kwata fainal a Champions League, bayan doke Bayern Leverkusen 3-1 gida da waje.
Arsenal ta yi nasarar cin ƙungiyar Jamus 2-0 ranar Talata a Emirates a wasa na biyu a gasar ta zakarun Turai, inda Eberechi Eze da Declan Rice suka ci mata kwallayen.
A makon da ya gabata a Jamus ranar Laraba, Bayern Leverkusen da Gunners suka tashi 1-1 a wasan farko zagayen ƴan 16 a gasar ta Champions League.
Da wannan sakamakon Gunners za ta buga wasan karshe a Carabao Cup ranar Lahadi a Wembley, ita kuwa Leverkusen za ta buga Bundesliga da Heidenheim ranar Asabar.
Arsenal na fatan lashe dukkan kofin gasar bana, wadda za ta fuskanci Southampton a FA Cup a makon farko a cikin watan Afirilu.
Gunners ce ta daya a kan teburin Premier League da tazarar maki tara tsakani da Manchester City ta biyu, kuma saura wasa bakwai ya rage mata ta kare wasannin Premier na kakar nan.