Arsenal ta dare teburin Premier League

Kungiyar Arsenal ta dare kan teburi na Premier League, bayan da ta ci Wolverhampton 2-0 a Molineux a wasan mako na 34.

Gunners ta ci kwalon farko ta hannun Leandro Trossard da kuma Martin Odegaard.

Hakan ya sa Arsenal ta koma ta daya da maki 74 a teburi, yayin da Manchester City ta koma ta biyu da maki 73, sai kuma Liverpool ta uku da maki 71.

Ranar Lahadi Liverpool za ta fafata da Fulham a wasan mako na 34 a Craven Cottage a babbar gasar tamaula ta England.

Ranar Laraba Bayern Munich ta fitar da Arsenal daga Champions League, bayan da ta ci 1-0 a Jamus, tun farko sun tashi 2-2 a Emirates a makon jiya.

Ranar Asabar Manchester City ta kai wasan karshe a FA Cup a Wembley, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea, wadda take ta tara a teburin Premier League.

Kofin Premier League ne kadai ya rage a gaban Arsenal, wadda rabon da ta dauka shekara 20, bayan da ba ta taba daukar Champions League ba.

A makon da ya gabata Manchester City ta dare teburi bayan caskara Luton Town 5-1, yayin da Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Aston Villa a Emirates, Crystal Palace ta ci Liverpool a Anfield.

Leave a comment