Arsenal ta ci gaba da zama a kan teburin Premier League

Liverpool da Arsenal sun tashi 1-1 a wasan mako na 18 a Premuer League ranar Asabar a Anfield.

Minti hudu da take leda Arsenal ta ci kwallo ta hannun Gabriel Magalhaes daga baya Mohamed Salah ya farke.

A kakar bara a Premier League Arsenal ta ci Liverpool 3-2 a Emirates ranar 9 ga watan Oktoban 2022.

A wasa na biyu a Anfield sun tashi 2-2 ranar 9 ga watan Afirilun 2023.

Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama ta daya a teburin Premier League da maki 40, Liverpool mai maki 39 ce ta biyu.

Aston Villa ma maki 39 ne da ita ta ukun taeburi, bayan wasa 18 da kowacce ta buga.

Wasannin da za a ci gaba a Premier League:

Ranar Talata 26 ga watan Disamba

  • Newcastle United da Nottingham Forest
  • Sheffield United da Luton Town    
  • Bournemouth da Fulham       
  • Burnley da Liverpool       
  • Manchester United da Aston Villa

Ranar Laraba 27 ga watan Disamba

  • Chelsea da Crystal Palace       
  • Brentford         da Wolverhampton
  • Everton da Manchester City  

Ranar Alhamis 28 ga watan Disamba

  • Brighton da Tottenham

Leave a comment