Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Arsenal ta bai wa Manchester City tazarar maki bakwai tsakani, sakamakon nasarar da ta je ta doke Brighton 1-0 ranar Laraba a gasar Premier League.
Arsenal, wadda ta buga wasa 30 ta zura ƙwallo a raga ta hannun Bukayo Saka tun a minti tara da take leda, hakan ya sa ta haɗa maki 67.
Ita kuwa City, wadda ta yi karawa 29 tana da maki 60, bayan tashi 2-2 da Nottingham Forest a Etihad a wasan da suka yi ranar Laraba.
Sauran sakamakon wasannin da aka buga a ranar Aaston Villa ta kwashi 4-1 a hannun Chelsea a Villa Park, ita kuwa Fulham ta yi rashin nasara 1-0 a gida a hannun West Ham United.
Sai kuma karawar da Newcastle ta ci Manchester United 1-0 a St James Park, duk da cewar ta karasa wasan da ƴan ƙwallo 10 a cikin fili, sakamakon da aka kori Ramsey.
Wannan shi ne karon farko da Micheal Carrick ya yi rashin nasara daga wasa takwas tun bayan da ya maye gurbin Ruben Amorim a matakin riƙon ƙwarya da cin wasa shida da canjaras ɗaya.
Sakamakon wasannin da aka buga a Premier League ranar Laraba:
- Newcastle 2 – 1 Man Utd
- Man City 2 – 2 Nottm Forest
- Aston Villa 1 – 4 Chelsea
- Brighton 0 – 1 Arsenal
- Fulham 0 – 1 West Ham
