Arsenal ba za ta bari Kiwior ya je aro a Janairu ba

Wasu rahotanni na cewar Arsenal ba za ta bari Jakub Kiwior ya je ya buga wasannin aro a wata kungiya a Janairu ba.

Dan kasar Poland ya buga wa Gunners wasu wasan tun bayan da ya koma Emirates daga Spezia, wanda ake hada shi wasa da William Saliba da kuma Gabriel Magalhaes.

Kiwior ya buga wasa uku a Premier League a bana, biyu daga ciki a mai tsaron baya daga hagu da karawa daya a Champions League.

Mai shekara 23 ya yi zaman benci karo 10, ya kuma shiga wasa daf a tashi a karawar da Arsenal ta ci Brighton 2-0 a gasar Premier League a karshen mako.

Bayan da Saliba da Gabriel na taka rawar gani a bana, hakan ya sa dan kwallon baya buga wasa sosai.

Rashin buga wasannin zai hana a gayyace shi buga Euro 2024, hakan zai zama koma baya mai girma a tare da shi.

Dalilin da wasu ke bayar da rahoton cewar zai koma wata kungiya a Janairu, domin yake buga wasanni sosai.

Leave a comment