Arsenal a shirye take ta yi cefane a Janairu – Arteta

Mikel Arteta ya ce a shirye ya ke ya shiga kasuwa, domin sayo karin ‘yan wasa idan har Arsenal za take cin karo da tasgaro kamar yadda ta yi baya.

Gunners za ta buga wasan mako na 19 a Premier League ranar Alhamis da West Ham United ba tare da ‘yan wasa biyar ba da ke jinya.

Arsenal ta kwan da sanin da zarar ta yi nasara a karawar za ta koma ta dayan teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Livepool, wadda za ta koma ta biyu.

‘Yan wasan da ke jinya sun hada da Thomas Partey da Jurrien Timber da Fabio Vieira da kuma Takehiro Tomiyasu, yayin da Kai Havertz ba zai buga wasa day aba, sakamakon katin gargadi biyar da ya karba kawo yanzu.

Arsenal ta kashe sama da £200 million ta sayo sabbin ‘yan kwallo kan fara kakar bana, ciki har da £105 million a sayen Declan Rice daga West Ham.

Dan kwallon tawagar Ingila ya koma Emirates tare da Havertz da Timber, kuma Gunners ta yi wadannan cefanen duk da kammala kakar bara a mataki na biyu, bayan da ta yi kwana 248 a kan teburi daga baya Manchester City ta karbe gurbin.

Kawo yanzu Arteta bai da tabbacin ranar da ‘yan wasansa za su kammala jinya, an kuma shiga lokacin da ake buga Premier League daf da daf.

Wannan lokacin shi ne mafi wuya a gasar Premier League, domin nan da nan sai a baka tazarar mai nisa, kuma lokaci ne da fitila ke haska wadda za ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar.

Saboda haka kungiya na bukatar fitattun ‘yan wasanta a tsaye cike da koshin lafiya.

Bayan nan za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka a Ivory Coast cikin Janairu zuwa Fabrairu, inda wasu kungiyoyin za su rasa manyan ‘yan kwallonsu.

Leave a comment