Argentina ta ci Brazil a wasan neman shiga kofin duniya

Argentina ta yi nasara a kan Brazil da ci 1-0 a Maracana a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

Ba a fara wasan a kan lokaci ba, bayan da aka samu hatsaniya tsakanin ‘yan kallo.

Argentina ta ci kwallon ta hannun mai tsaron baya, Nicolas Otamendi a minti na 63.

Nasarar da Argentina ta yi ya sa ta ci gaba da zama a matakin farko a teburin Kudancin Amurka da maki 15 a wasa shida.

Brazil, wadda karo na uku ana doke ta a wasannnin neman zuwa gasar da Amurka da Canada da Mexico za su karbi bakunci, tana ta shidan teburi da maki bakwai daga wasa shida.

Tun kan fara karawar ta hamayya an ga ‘yan sandan Brazil suna dukan magoya bayan Argentina, wadanda suka rufe wata mashiga a filin.

Hakan ya sa magoya bayan suka kai korafi daf da tawagar Argentina, inda mai tsaron raga, Emi Martinez ya yi kokarin haurawa, domin ya hana ‘yan sanda dukan magoya bayan Argentina.

Hakan ya sa Lionel Messi ya umarci ‘yan wasa su koma dakin hutu, har sai an samu kwanciyar hankali a filin.

Bayan da komai ya natsa ne tawagar Argentina ta koma fili aka fara take wasan.

Argentina ce ta lashe kofin duniya a 2022 a Qatar, kuma na uku jimilla kenan.

Leave a comment