Ancelotti ya zabi Real Madrid maimakon horar da Brazil

Carlo Ancelotti ya tsawaita kwantiragin ci gaba da horar da Real Madrid zuwa karshen Yunin 2026.

Hakan ya kawo karshen batun da ake cewar tawagar kwallon kafar Brazil na son bai wa kocin aikin jan ragamarta

Kamar yadda Real Madrid ta fitar da wata sanarwa ‘’Real Madrid da Carlo Ancelotti mun cimma yarjejeniyar ci gaba da aiki tare zuwa 30 ga watan Yunin 2026.’’

Tun cikin watan Yuli aka bayar da sanarwar cewar mai shekara 64, zai zama mai horar da Brazil daga waje na farko da za a bai wa aikin da zarar kwantiraginsa ya kare da kungiyar Spain.

Hakan ya sa tawagar Brazil ta bai wa Fernando Diniz aikin rikon kwarya, kafin daga baya Ancelotti ya fara kai kasar gasar Copa America.

A lokacin da Ednaldo Rodriguez, yake shugaban hukumar kwallon kafar Brazil ya tattauna da Ancelotti, wanda ya sanar cewar daga Real Madrid zai yi ritaya daga horar da tamaula.

A karkashin Diniz, Brazil ba ta taka rawar gani, wadda take ta shida a teburin Kudancin Amurka a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

Ancelotti bai taba furka cewar ya amince zai karbi aikin kociyan Brazil ba.

Idan ka kwatanta da kwazon Brazil, Real Madrid tana jan ragamar teburin LaLiga da maki iri daya da na Girona.

Haka kuma ta kai zagaye na biyu a Champions League, bayan da ta lashe dukkan wasa shida a cikin rukuni.

Ancelotti fitatcen kociya ne a duniya, wanda ya dauki kofin Champions League hudu – guda biyu a AC Milan da wasu biyun a Real Madrid.

Ya lashe kofin babbar gasar tamaula a Spain da Real Madrid da Milan a Italy da Chelsea a England da Bayern Munich a Germany da kuma a France da Paris Saint-Germain.

Leave a comment