Ancelotti na sa ran a Janairu Vinicius zai koma wasa

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce yana sa ran Vinicius Junior da Eduardo Camavinga za su koma taka leda cikin watan Janairun 2024.

Vinicius yana jinya tun bayan da ya ji rauni a wasan Brazil da Colombia a neman shiga gasar kofin duniya da suka yi a watan jiya.

Shi kuwa Camavinga dan kwallon tawagar France bai yiwa Real Madrid wasa uku ba, sakamakon rauni a gwiwa.

Wasan farko da Real Madrid za ta buga a 2024, shi ne wanda za ta karbi bakuncin Real Mallorca ranar 3 ga watan Janairu.

Vinicius ya ciwa Real Madrid kwallo shida daga wasa 13 a bana a kungiyar da ke jan ragamar teburin LaLiga kawo yanzu.

Ancelotti ya yi watsi da batun da ake cewar Jude Bellingham na bukatar likitoci su yi masa tiyata.

Real Madrid mai maki 38 za ta iya bayar da tazarar maki uku ranar Asabar idan ta je ta doke Real Betis a wasan LaLiga.

Ranar Lahadi Girona, wadda take ta biyu a teburi da maki iri daya da na Real Madrid za ta je gidan Barcelona, wadda take mataki na ukun teburi..

Leave a comment