Ana ta cece-kuce kan bai wa Brys kociyan Cameroon

Hukumar kwallon kafa ta Cameroon ta bayyana bacin rai, bayan da ofishin ministan wasanni ya sanar da nada Marc Brys a matakin sabon kociyan Indomitable Lions.

Mai shekara 61dan kasar Belgium, wanda a baya ya horar da OH Leuven zai maye gurbin tsohon dan wasan Liverpool da West Ham United, Rigobert Song.

Tsohon dan wasan Barcelona da Inter Milan da Chelsea, Samuel Eto shi ne shugaban hukumar kwallon kafar Cameroon tun daga Disambar 2021.

Ofishin ministan wasannin ya sanar cewar Brys zai yi aiki tare da Joachim Mununga da kuma Giannis Xilouris a matakin masu taimaka masa, amma ba wani karin bayi kan kunshin kwantiragin.

An bai wa Song aikin horar da Indomitable Lions cikin 2022 lokacin da shugaban Cameroon, Paul Biya ya bayar da umarni, sai dai yarjejeniyarsa ta kare a watan Fabrairu.

Song ya ja ragamar Cameroon zuwa gasar kofin duniya a 2022 a Qatar, inda Indomitable Lions ta ci Brazil, amma ta kasa haura karawar cikin rukuni.

A cikin shekarar nan Nigeria ta fitar da Cameroon daga gasar cin kofin Afirka a zagayen ‘yan 16 da aka yi a Ivory Coast.

Leave a comment