Gavi zai yi jinyar wata takwas zuwa 10

Dan kwallon Barcelona, Gavi ya ji ciwo a gwiwar kafarsa a lokacin da yake buga wa Sifaniya tamaula.

Gavi, mai shekara 19, an fitar da shi daga filin yana kuka ranar Lahadi, bayan da Spaniya ta doke Georgia 3-1 a wasan neman shiga Euro 2024.

watakila Gavi y agama buga tamaula a kakar nan sai badi, ba zai yi wa Sifaniya Euro 2024 ba, da kyar idan zai je gasar Olympic da za a yi a birnin Paris a 2024.

Barcelona ta tabbarar da raunin bayan da ta kammala auna girman ciwon ranar Litinin, ana sa ran zai ji jinyar wata takwas zuwa tara.

Gavi ya yiwa Barcelona wasa 111 da cin kwallo bakwai da bayar da 12 aka zura su a raga.

Haka kuma ya buga wa Sifaniya fafatawa 27 da cin kwallo biyar.

Leave a comment