Ana ci gaba da sayar da tikitin Euro 2023 zango na biyu

Ranar Litinin an ci gaba da sayar da tikitin kallon gasar nahiyar Turai, Euro 2024 da Jamus za ta karbi bakunci.

An samar da tikiti miliyan daya a wasannin cikin rukuni, bayan da aka samu tawaga 21 da suka samu gurbi kai tsaye.  

Kowacce hukumar kwallon kafa da za ta buga gasar tana da tikiti 10,000 a wasa uku da za ta yi a cikin rukuni.

Za a fara gasar kofin nahiyar Turai daga 14 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Yulin 2024.

Farashin tikitin ya kama daga Yuro 30 zuwa 200, amma a wasan farko da za a fara tsakanin Germany da Scotland zai kama daga Yuro 50 zuwa 600.

An kuma samu ragowar tikitin farko da aka fara sayarwa, yayin da ake sa ran kara fitar da wasu tikitin ga kasa ukun da za su samu gurbin shiga gasar nan gaba.

Leave a comment