An yi waje da Nadal daga Italian Open na bana

Fatan da Rafael Nadal keda shi na lashe gasar kwallon tennis ta Italian Open karo na 11 ya zo karshe, bayan da Hubert Hurkacz ya fitar da shi a Rome.

Ranar Alhamis, Nadal ya sa kaimi ya fitar da Zizou Bergs, ya kai zagayen gaba a gasar da rabonda ya lashe tun 2021.

To dai dan kasar Spain ya yi rashin nasara a hannun Hurkacz da ci 6-1, 6-3 a karawar da wsu ke cewa watakila ita ce ta karshe da Nadal ya buga ta Italy.

Nadal mai Grand Slam 22 ya ci karo da koma baya, sakamakon jinya da ya yi ta fama.

A gasar mata kuwa, Iga Swiatek ta kai matakin ‘yan 16, bayan da ta caskara Yulia Putintseva.

Swiatek za ta fuskanci Angelique Kerber a wasan gaba, yayin da Naomi Osaka, wadda ke taka rawar gani a bana ta yi waje da Daria Kasatkina da ci 6-3, 6-3.

Leave a comment