An yi waje da Man United a Champions League

An fitar da Manchester United a Champions League, kuma ba za ta je Europa League ba, sakamakon da Bayern Munich ta doke 1-0 a Old Trafford.

Tun kan wasan ranar Talata Bayern Munich ta kai gurbin zagayen gaba, wadda ta hada maki 16 a rukunin farko.

Kungiyar Jamus ta yi wasa 40 a cikin rukuni a gasar zakarun Turai ba tare da rashin nasara ba.

Copenhagen ce ta biyu a rukunin farko, wadda ta ci Galatasaray 1-0 ta hada maki takwas.

Sai dai kungiyar Turkey ta samu shiga wasannin Europa League, Man United ce ta karshe a rukunin.

Union Berlin ta kare kakar bana karon farko da ta fara Champions League ba tare da nasara ba a cikin rukuni.

Kungiyar Jamus ta yi rashin nasara da ci 3-2 a gida a hannun Real Madrid, ta yi ban kwana da wasannin, sai dai ta mayar da hankali a Bundesliga ko ta koma gasar zakarun Turai a badi.

Tuni Real Madrid ta kai zagayen gaba tun kan ranar Talata, wadda yanzu ta hada maki 18 da cinye dukkan fafatawar cikin rukuni na uku.

Napoli ce ta biyu mai maki 10, wadda ta doke Sporting Braga 2-0, sai dai Braga za ta buga Europa.

Arsenal wadda ta dan kwana biyu rabonta da Champions League ta kai zagaye na biyu, duk da tashi 1-1 a gidan PSV Eindhoven.

Kungiyar Netherlands ce ta biyu da maki tara a rukuni na biyu.

Leave a comment