An yi wa FA Cup kwaskwarima daga 2024/25

An tabbatar da yi wa Emirates Cup kwaskwarima daga kakar 2024/25, kamar yadda mahukuntan gasar suka sanar ranar Alhamis.

Daga yanzu an daina maimata wasa idan an tashi ba a samu gwani ba, a ranar za a yi gubun fenariti, domin kungiyoyi su samu damr hutu, kafin gasar zakarun Turai da itama aka sauya mata fasali daga kaka mai zuwa.

Ya zama wajibi a tantance kungiyar da za ta kai zagayen gaba a wasa, ko dai a yi karin lokaci daga nan a yi bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Za a dui na yin wasa a tsakiyar mako, kenan za a yi wasannin ne idan babu karawar Premier League a karshen mako, amma daga zagaye na biyar. A karawar zagaye na hudu za a iya a tsakiyar mako ko kuma ranar Laraba.

Haka kuma kungiyoyin Premier League za su samar da £33 millions domin tallafawa kananan kungiyoyin dake buga gasar England, wato kari kan £100 million dake bayar wa duk kaka

Wannan sauyi zai fara daga kakar badi zuwa shekara shida daga nan a sake ganin ko da wasu sauye-sauye da za a bukata.

Ranar Asabar za ta buga daf da karshe tsakanin Manchester da Chelsea a FA Cup, yayin da Coventry City da Manchester United za su kece raini ranar Lahadi da za a buga dukkan karawa a Wembley.

Leave a comment