An tuhumi Arteta saboda kalamai kan hukuncin VAR

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Mikel Arteta kan kalaman da ya yi, bayan wasa da Newcastle a farkon watan nan.

Newcastle United ce ta doke Arsenal 1-0 a St James Park ta takawa Gunners burki, wadda ba a ci ba a wasa 10 da fara Premier League a bana.

An ci karo da takaddama, inda Arteta ya kwatanta VAR da barin kwallon da aka ci Arsenal da cewar ‘’Abin kunya ne.’’

Anthony Gordon ne ya ci kwallon, wanda tun farko aka ce an yi ture, kafin nan ana zargin kwallon da Joe Willock ya bugo ta fita waje.

Alkalan da suka ja ragamar sun yi ta duba VAR karo da dama kan ko kwallon da Willock ya bugo ya fita waje, ko Joelington ya yi ture, sannan ko Gordon ya yi satar gida, amma ba wani laifi da aka gani.

Kungiyar Arsenal ta fitar da jawabin cewar tana goyon dukkan kalaman da Arteta ya yi.

Dan kasar Sifaniya ya sanar cewar aikinsa ne ya kare Gunners, sannan ya dace ya fadi abinda aka yi musu na rashin kyautawa.

Hukumar ta bai wa Arteta nan da ranar Talata domin ya kare kansa.

Arsenal tana mataki na uku a kan teburin Premier League da maki 27 iri daya da na Liverpool ta biyu.

Manchester City mai rike da kofin bara ita ce da daya mai maki 28.

Leave a comment