An tsare Rubiales bisa zargin rashawa da cin hanci

An kama tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Spain, Luis Rubiales ranar Laraba kan zargin rashawa da cin hanci.

Daga baya an sake shi, bayan da aka tsara shi a birnin Madrid.

Ana zargin ya karbi wani kaso mai tsoka lokacin da aka kulla yarjejeniyar buga Spanish Super Cup a Saudi Arabia.

Masu shigar da kara na fatan za a daure Rubiales shekara biyu da rabi – zargin da musanta hannu a ciki.

Bayan da ya sauka a jirgin sama, sai jami’ai suka saka shi a wata bakar mota tare da jami’an tsaro, daga baya aka sake shi bayan da ya amince zai halarci kotu ranar Alhamis.

Aa watan jiya aka yi bincike a gidan Rubiales lokacin da yake Dominican Republic.

Haka kuma ana jiran ranar da za a gurfanar da Mr Rubiales gaban kotu, bisa zargin sumbatar Jenni Hermoso a lebe a lokacin gasar cin kofin duniya a Australia da New Zealand.

Dalilin haka ne ya sa Mr Rubiales ya ajiye aikin shugabancin hukumar kwallon kafar Spain..

Leave a comment