An tashi 3-3 tsakanin Real da Man City a Champions League

Real Madrid ta tashi 3-3 da Manchester City a wasan farko zagayen quarter finals da suka kece raini ranar Talata a Santiago Bernabeu.

City ce ta fara cin kwallo da fara wasa ta hannun Bernardo Silva a bugun tazarar daga nan ta yi gaba da 3-2, inda Josko Gvardiol ya kara na biyu a minti na 71, bayan da Phil Foden ya ci na uku a Spain.

Sai dai Real Madrid, wadda kociyanta Carlo Ancelotti ya ja ragamar Champions League na 200 ta saka kaimi a fafatawar ta hamayya.

Real ta fara farke kwallo ta hannun Ruben Dias, wanda ya ci gida, sai Rodrygo ya kara na biyu, Real ta zama tana gaba da cin 2-1 haka aka je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne City ta farke ta kara na uku daga baya Real ta zura na uku a ragar City ta hannun Federico Valverdo.

Kenan za su buga wasa na biyu a England a zagayen daf da na kusa da na karshe ranar Laraba 17 ga watan Afirilu.

Manchester City mai Champions daya da ta lashe a bara, ita ce ta yi da Real Madrid mai kofin zakarun Turai 14.

Leave a comment